Tsohon Ministan Sadarwar Najeriya kana mai neman tsayawa takarar gwamna a jihar Gombe a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Farfesa Isa Ali Pantami, ya sha alwashin ɗaukar duk wani mataki da ke bisa doka wajen ƙalubalantar yadda aka fitar da ɗan takarar gwamnan jihar na zaɓen baɗi.